Wakilin na kasar Sin ya bayyana haka ne a wajen taron kwamitin sulhu na MDD da aka kira a jiya Alhamis don tattauna batun Syria.
Ma Zhaoxu ya ce, kasarsa na tausayawa jama'ar Syria, la'akari da wahalhalun da suka sha sakamakon wutar yaki. Sa'an nan a ganin kasar Sin, neman daidaita yanayin a siyasance ita ce hanya daya tak da bangarori masu ruwa da tsaki za su iya bi. Matakin da ake bukatar dauka a yanzu shi ne, tabbatar da komawa teburin sulhu bisa shiga tsakani da MDD ke yi, da kokarin neman wata manufa da dukkan bangarorin kasar za su amince da ita. Yana mai cewa, ta wannan hanya ne za a samu damar fitar da jama'ar kasar daga mawuyacin halin da suke ciki. (Bello Wang)