in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Malaman makarantu da dalibai a Najeriya sun yi Allah wadai da yin garkuwa da mata 'yan makaranta
2018-02-27 08:47:54 cri
Hadaddiyar kungiyar malaman makaranta da dalibai ta Najeriya ta yi Allah wadai da garkuwar da kungiyar 'yan ta'adda ta yi da dalibai mata 'yan makarantar sakandaren kimiyya da fasaha ta Dapchi a jahar Yobe dake shiyyar arewa maso gabashin kasar a ranar 19 ga watan nan na Faburairu.

Lai Mohammed, ministan yada labarai da raya al'adu na Najeriya ya ce, gwamnati ta umarci jami'an 'yan sanda da na kare fararen hula a jahar Yoben da su hanzarta tura jami'ansu zuwa dukkan makarantun jihar domin tabbatar da tsaro. Ya ce gwamnati ta dauki dukkan matakan da suka dace domin ceto 'yan matan da aka sace domin dawo da su zuwa ga iyayensu lami lafiya, ya kara da cewa, hukumomin tsaron kasar na ci gaba da daukar matakan gano inda mata 'yan makarantar suke. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China