Kakakin sojin saman Najeriya Olatokunbo Adesanya, ya ce, dakarun sojin saman na ci gaba da aikin binciko yaran ba dare ba rana.
Ana zargin kungiyar 'yan ta'adda na Boko Haram ne suka yi garkuwa da yaran, bayan wani harin da suka kaddamar a makarantar sakandaren 'yan mata ta kimiyya da fasaha dake Dapchi a jahar Yobe, shiyyar arewa maso gabashin kasar a ranar Litinin din da ta gabata.
Gwamnatin Najeriya ta sanar a ranar Lahadi cewa, ba'a ga yara mata 'yan makarantar kimanin 110 ba tun bayan harin da mayakan suka kaddamar.
Adesanya ya ce, a bayyane take dakarun sojojin na ci gaba da kara kokari tare da hadin gwiwar sauran jami'an tsaro domin binciko 'yan matan.
Kakakin sojojin ya bayyana cewa, gwamnatin kasar ta daura aniyar kubutar da dukkan yaran 'yan makarantar da suka bace. (Ahmad Fagam)