in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin Najeriya sun hallaka mayakan Boko Haram 5
2018-02-25 12:19:46 cri
Rundunar sojin Najeriya tace ta samu nasarar hallaka mayakan Boko Haram 5 a lokacin da dakarun sojin suka kaddamar da samame a kokarin da suke na kakkabe dukkan maboyar mayakan 'yan ta'addan daga shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Onyema Nwachukwu, mai magana da da yawun rundunar sojin dake Maiduguri, babban birnin jahar Borno, a arewa maso gabashin kasar ya bayyana cewa, an harbe mayakan na Boko Haram ne har lahira a wata maboyarsu dake Parisu, a kusa da dajin Sambisa a Juma'ar data gabata.

Kakakin rundunar sojin ya ce, sojojin sun ceto fararen hula 3 wadanda 'yan Boko Haram din suka yi garkuwa da su a lokacin samamen da sojojin suka kaddamar a yankin.

A cewar Nwachukwu, da ma dakarun sojin Najeriyar suna hakon mayakan na Boko Haram ne tun a ranar Alhamis din da ta gabata.

Boko Haram ta fara kaddamar da hare haren ta'addanci ne tun a shekarar 2009, a fafutukar da take na kafa daular Musulunci a shiyyar arewa maso gabashin kasar, inda ta yi sanadiyyar kashe rayukan jama'a sama da 20,000, ta kuma raba miliyoyin mutane da muhallansu.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China