in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijeriya ya ce za a tura karin dakarun da za su nemo 'yan matan da suka bata
2018-02-24 12:26:51 cri

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya ce zai tura karin dakaru da jirgin sa ido domin binciko 'yan matan sakandare da suka bata, bayan an yi zargin kungiyar Boko Haram da kai hari kan makarantarsu dake jihar Yobe na arewa maso gabashin kasar a ranar Litinin da ta gabata.

Cikin wata sanarwa, Shugaba Buhari ya tabbatarwa iyalan 'yan matan cewa, za a yi dukkan mai yuwa na ganin an kai musu dauki, domin za a umarci dakarun kasar su sanya ido kan duk wata zirga-zirga a duk fadin yankin ba dare-ba rana, domin samo 'yan matan.

A ranar Alhamis da ta gabata ne gwamnatin kasar ta ce ba ta da tabbacin adadin 'yan matan da suka bata, inda ta nemi a kara mata lokaci don tantance al'amarin.

Muhammadu Buhari ya bayyana al'amarin a matsayin iftila'in da ya shafi baki dayan kasar, yana mai cewa daukacin al'ummar kasar na zaman iyalan 'yan matan. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China