Babban jami'in sojin ya ce makasudin kafa wannan rundunar soji shi ne, domin daukar matakan shawo kan dunbun kalubalolin tsaro da kasar ke fuskanta.
Buratai ya ce, an kafa rundunar sojin ne bayan lura da girman matsalar barazanar tsaro dake damun jahar da ma illahirin yankunan shiyyar arewa maso yammacin Najeriyar.
Ya ce tuni majalisar gudanarwar sojojin kasar ta amince da kafa wannan runduna karkashin dokar yaki ta 2016.
Jami'in sojin yace kafa wannan runduna yana daga cikin dabarun da za su taimaka wajen tunkarar kalubalolin tsaro dake addabar kasar.
Ya ce musamman, jahar na fama da matsalolin barayin shanu, da 'yan fashi da makami da masu dauke da makamai, da masu aikata muggan laifuka a kan iyakokin jahar.(Ahmad Fagam)