in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani dan kunar bakin wake ya kai hari Jami'ar Maiduguri dake Nijeriya
2018-02-21 12:35:56 cri

Rundunar 'yan sandan Jihar Borno ta tabbatar da harin da wani dan kunar bakin wake ya kai Jami'ar Maiduguri babban birnin Jihar dake yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

Kakakin rundunar Joseph Kwaji, ya shaidawa manema labarai a Maiduguri cewa, dan kunar bakin waken ya tada bam din dake daure a jikinsa ne a jikin katangar jami'ar a ranar Litinin.

Joseph Kwaji wanda ya ce baya ga dan kunar bakin waken, babu wanda harin ya rutsa da shi, ya ce tuni jami'an tsaro suka killace wajen.

Jami'in ya ce ana zargin kungiyar Boko Haram da kai harin, a wani yunkurin mayakanta na kutsawa jami'ar.

Cikin shekarar da ta gabata, jerin hare-haren da aka kai Jami'ar ta Maiduguri ya yi sanadin mutuwar gomman mutane ciki har da wani shehun malami. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China