Shugaban kwamitin shirya wasannin Olympics na duniya Thomas Bach, ya sanar da rufe taron a wajen bikin da aka gudanar a jiya. Manyan kusoshin kasa da kasa da suka halarci bikin rufe taron sun hada da Madam Liu Yandong, wakiliyar musamman ta shugaban kasar Sin Xi Jinping, kana mataimakiyar firaministar kasar Sin.
Daga bisani, mista Chen Jining, magajin birnin Beijing, wanda zai karbi bakuncin taron wasannin Olympics na lokacin sanyi a karo mai zuwa, ya karbi tutar wasannin Olympics a madadin birnin. Haka kuma, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya isar da sakon gayyata ga jama'ar kasa da kasa ta wani bidiyon da aka dauka, inda ya ce, "bari a hadu a birnin Beijing a shekarar 2022", lokacin da za a gudanar da taron wasannin Olympics na lokacin sanyi a karo mai zuwa. Kana ban da birnin Beijing, za a gudanar da gasanni daban daban a garin Zhang-Jia-Kou na kasar Sin a taron wasanni Olympics na lokacin sanyi mai zuwa.(Bello Wang)