in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasan rawar motsa jiki
2018-02-02 06:35:16 cri


Yanzu da an ambaci kalmar "rawar motsa jiki" ko kuma "dance sport" a Turance, ana iya fahimtar wasu nau'oin rawar musamman guda 10 da ake yi cikin daki, wadanda za a iya gudanar da gasanni a kansu. Dukkan wadannan rawa suna bukatar mutane 2 su yi rawa tare, wato namiji daya da mace daya. Sa'an nan ana iya kasa rawar guda 10 zuwa gidaje 2, wato iri ta "Standard" da kuma ta "Latin Style". Rawar nau'i 2 sun sha bamban da juna, a fannin fasahohin taka rawa, da kide-kiden da ake sakawa yayin da ake rawar, gami da tufafin da ake sanyawa. Amma manufar da alkalan wasa suke bi wajen ba da maki ga masu taka rawa iri daya ne, wato ana mai da hankali kan kwarewar da aka nuna wajen sarrafa jiki, da kyan ganin rawar da aka taka.

Asalin rawar motsa jiki shi ne rawar kulla hulda tsakanin mutane, wadda ta yi farin jini a kasashen Turai, musamman ma kasar Faransa a karni na 16. Mutanen da suka taka wannan irin rawa dattawa da 'yan mata masu matsayi ne, wandada suka saba da taka rawa mai kyan gani a lokacin da suke halartar bukukuwa daban daban.

Zuwa karshen karnin 17, sarkin kasar Faransa na lokacin Louis na 14 ya kafa wata "Cibiyar Nazarin Kide-kide da Rawa", inda masanan ilimin fasahohin al'adu suka tabbatar da ka'idojin da ake bi wajen taka rawa daban daban. Haka kuma a lokacin ne, aka cire rawar "Ballet" daga rawar da ake takawa a yau da kullum, domin mai da ita wata rawar musamman da kwararrun masu rawa ke takawa a kan dandali.

Daga bisani, an dinga gyaran motsin rawa, da kide-kiden rawar, har zuwa karni na 19, rawar ta yi farin jini sosai tsakanin jama'ar nahiyar Turai da ta Amurka. Yadda ake samun mutane da yawa masu halartar wasan taka rawa, ya sa aka fara gudanar da gasanni a wannan fanni, inda babbar gasar taka rawa ta kasa da kasa ta farko ta gudana a shekarar 1909.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China