in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da ginin dake alamta gasar Olympic ta PyeongChang
2018-02-07 19:45:10 cri

An kaddamar da ginin dake alamta shirin bude gasar Olympic ta lokacin hunturu a kauyen wasannin dake birnin PyeongChang, wurin da za a gudanar da gasar ta Koriya ta kudu. An dai yiwa gasar ta bana lakabin "Gina gada" wanda aka rubuta a kan ginin dake kauyukan Olympic dake Gangneung da kuma PyeongChang.

Mashirya gasar PyeongChang ta 2018 na ganin cewa "ginin mai kama da gada na alamta shirin PyeongChang na tabbatar da wanzuwar hadin gwiwa da sauran kasashe, domin samar da duniya mai inganci ga kowa ta hanyar wasanni.

Ana fatan za a baiwa 'yan wasa da jami'an su damar sa hannu ko rubuta sakwannin su kan gadar mai tsawon mita 7 a kasa da mita 3 a tsaye. Daga bisani kuma za a dauke gadojin zuwa filin wasanni dake birnin PyeongChang da Gangneung, inda za a baje kolin su ga masu sha'awar kallo har zuwa karshen gasar da za gudanar.

Da yake tsokaci game da hakan, yayin kaddamar da ginin shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa Thomas Bach, ya ce ginin wanda ke alamta gada na bayyana bukatar da ake da ita, ta hada gwiwa da juna a wannan lokaci da duniya ke cikin wani hali na raunin dangantaka. Ya ce hakan na daya daga dalilan da suka sanya PyeongChang ta gayyaci 'yan kallo daga sassan duniya daban daban da 'yan jaridu, da 'yan wasa domin sada zumunta tsakanin kasashe daban daban.

A nasa bangare, shugaban kwamitin tsare tsare na gasar Mr. Lee Hee-beom, ya ce "gasar PyeongChang ta 2018 gasa ce ta wanzar da zaman lafiya. Kuma kaddamar da ginin dake alamta hakan, alama ce ta zahiri dake gabatar da wannan sako ga sassan duniya.

An hana 'yan wasa da kociya 15 daga Rasha shiga gasar PyeongChang 2018

Kwamitin shirya gasar Olympic na kasa da kasa IOC, ya dakatar da gayyatar da aka yiwa sama da 'yan wasan 13, da wasu kociya biyu zuwa gasar PyeongChang, duk da cewa an dage zargin da aka yi masu na mu'amala ko tallafawa masu mu'amala da kwayoyi masu kara kuzari.

A ranar 2 ga watan Fabarairu na bana, kwamitin wasannin Olympic na kasar Rasha ROC, ya gabatar da jerin sunayen mutane 15, wadanda aka dagewa takunkumin shiga harkokin wasannin kasar, bayan kotun hukunta harkokin wasanni ta CAF ta wanke su. Cikin mutanen akwai 'yan wasa 13 da wadanda suka yi ritaya 2, wadanda kuma sun halarci gasar birnin Sochi ta shekarar 2014, kuma har yanzu ake damawa da su a harkokin wasanni.

Sashen lura da gabatar da takardun gayyata na IOC ne dai ya bayyana bukatar dakatar da gayyatar mutanen 15, duk da cewa hukumar ROC ta Rasha ta dage musu takunkumi na zargi.

Sashen ya ce har yanzu akwai sauran bincike kan mutanen, kuma dage musu takunkumin da aka yi, ba ya nuna ba su keta dokokin hana ta'ammali da kayan kara kuzari ba. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China