in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasannin lokacin sanyi masu ban sha'awa
2018-02-22 15:43:10 cri


Game da tarihin wasannin lokacin sanyi, ko kuma wasanni masu alaka da kankara, yanzu mun san an fara gudanar da wasannin ne a wasu yankuna masu sanyi. A wadannan wurare, idan lokacin sanyi ya zo, a kan samu saukowar kankara mai taushi, kana yanayi mai sanyi na sanyawa kankara da ta sauka kasa ba za ta narke ba. Maimakon haka za ta dinga taruwa a kasa, har ma ta rufe dukkan hanyoyi. Wani lokaci ma, sai a ga kankara ta toshe kofar gida.

Don daidaita matsalar kankara, wadda take hana mutane yin amfani da hanyoyi, an kirkiro wasu na'urorin sufuri na musamman, irinsu "sledge", "ski" da "skates", wadanda suke baiwa mutane damar zamiya a kan kankara cikin sauki, ba tare da jin rauni ba.

Bayan da aka kirkiro wadannan na'urorin sufuri a kan kankara, aka kuma samu fasahohin sarrafa na'urorin, sannu a hankali an fara gudanar da wasanni don gwada fasahar zamiya kan kankara. Ta haka aka fara samun wasannin kankara daban daban. Kuma yawancinsu ana gudanar da su ne a waje cikin lokacin sanyi, yayin da wasu daga cikinsu, ga misali, wasan hockey a kan kankara, da wasan gudun kankara, ana gudanar da su ne a cikin dakunan kankara, inda ake yin amfani da wasu injuna domin samar da kankara da ake bukata.

Wannan fasaha ta sa ana iya gudanar da wasannin a duk lokaci cikin ko wace shekara. Ko a lokacin zafi ma, ba za a daina gudanar da wasannin ba, tun da za a iya ci gaba da samar da kankara cikin dakunan na musamman.

A nan kasar ta Sin, an fara shiga wasannin kankara da wuri, ganin yadda kasar take da makeken yankin da ya kasance wurin da lokacin sanyinsa yana da tsayi. A da can, Sinawa sun taba yin amfani da wasannin kankara a matsayin wata dabarar atisayen sojoji, domin yakin da aka yi a arewacin kasar na bukatar sojoji su koyi fasahar yin amfani da takalmar wasan kankara. Domin biyan wannan bukata, sarkin kasar ya taba shirya wasu gasannin wasan kankara a shekaru fiye da 100 da suka wuce.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China