in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da gasar wasannin Olympics na lokacin hunkuru na PyeongChang karo na 23
2018-02-10 13:39:00 cri

A jiya Juma'a 9 ga wata, aka kaddamar da gasar wasannin Olympics na lokacin hunkuru na PyeongChang karo na 23 a filin wasa na Olympics na birnin PyeongChang dake kasar Koriya ta Kudu.

A matsayin gasa ta koli na wasannin lokacin hunkuru ta duniya, gasar wasannin Olympics na lokacin hunkuru a wannan karo ta jawo 'yan wasa kimanin dubu 3 daga kasashe da yankuna 92 na duniya. A gun bikin bude gasar, tawagar 'yan wasan kasar Koriya ta Arewa da ta Koriya ta Kudu sun jinjina tutar zirin Koriya da shiga filin wasan. A matsayin kasa mai daukar bakuncin gasar a wannan karo, kasar Koriya ta Kudu ta tura tawagar 'yan wasa da ya kasance mafi yawa a tarihi, wato yawan 'yan wasanta ya kai 144. Kuma kasar Koriya ta Arewa ta tura 'yan wasa 22. Koriya ta Arewa data Kudu zasu hadu da juna yayin halartar gasar wasan kwallo a kan kankara tare.

Shugaban kwamitin wasannin Olympics na duniya Thomas Bach ya yi jawabi cewa, kafa tawagar hadin gwiwa ta Koriya ta Arewa da ta Kudu ya burge jama'a sosai, ya shaidawa duniya alamar shimfida zaman lafiya.

A matsayinta na kasa mai daukar bakuncin gasar wasannin Olympics a karo mai zuwa, kasar Sin ta tura 'yan wasa 82 wadanda zasu halarci wasanni 55.

Za a rufe gasar wasannin Olympics na lokacin hunkuru a wannan karo a ranar 25 ga wannan wata. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China