in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta duniya a London
2018-02-07 19:43:35 cri
Hukumar shirya gasar wasanni ta Birtaniya ta sanar cewa, za a gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta duniya ta London 2018, inda za'a gudanar a katafaren filin wasa na London Olympic Stadium tsakanin 14-15 ga watan Yulin shekarar 2018 da muke ciki.

Sanarwar ta ambato cewa, manyan kungiyoyin wasanni na kasashen duniya 8 ne zasu halarci gasar, da suka hada da Amurka, Birtaniya, Poland, Sin, Jamus, Faransa, Jamaica da Afrika ta kudu, inda zasu fafata don daukar kofin duniya.

Kowace kasa zata gwada sa'arta ta neman lashe kyautar dala miliyan biyu a wasannin da za'a buga na tsawon wuni biyu.

Za'a zabo namiji guda da mace guda daga kowace kasa a dukkan wasannin da za'a gudanar a zagayen karshe na wasannin.

Sebastian Coe, shugaban hukumar shirya wasannin motsa jiki ta duniya, yace yana goyon bayan wasa da za'a gudanar dari-bisa-dari.

Coe yace, wannan na daya daga cikin muhimmin tunani a fagen wasannin motsa jiki, kuma dole ne a godewa hukumar shirya wasannin motsa jiki ta Birtaniya, da magajin garin Landan, saboda shirwa wasan da kuma karbar bakuncinsa.

Yace, "Muna da hanyoyi 8, manyan kasashe 8, tawagar 'yan wasa 8, kuma zasu halarci jerin wasannin don neman lashe kyautar. Wannan wani cigaba ne kuma abun farin ciki ne matuka a fagen wasanni harma ga masu sha'awar wasannin".(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China