in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump da Putin sun ce harkokin sadarwa na sojoji ya inganta a Syria
2017-11-12 12:40:57 cri
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, sun bayyana gamsuwa game da kyautatuwar yanayin sadarwa a tsakanin jami'an sojinsu dake kasar Syria, wanda a cewarsu ya samu ingantuwa a yakin da suke yi da mayakan kungiyar masu da'awar kafa daular musulunci IS musamman a 'yan watannin nan.

A wata sanarwar hadin gwiwa da shugabannin biyu suka fitar a ranar Asabar a lokacin halartar taron hadin gwiwa kan tattalin arziki na shugabannin yankin Pacific wato (APEC) a birnin Da Nang, na kasar Vietnam, shugabannin biyu sun tabbatar da cewa suna samun galaba a yakin da suke yi da IS a Syria.

A cewar sanarwar, wadda aka wallafa ta a shafin intanet na hukumar harkokin wajen Amurka, shugabannin sun amince za su bude wata hanyar sadarwa tsakanin sojojin kasashen biyu domin hakan zai taimaka wajen tsaron lafiyar sojojin na Amurka da Rasha a fafutukar da suke na yaki da IS har zuwa lokacin da za su samu cikakkiyar galaba a kansu.

Haka zalika sanarwar shugabannin biyu ta bayyana cewa, matakin soji ba zai iya kawo karshen rikicin Syria ba, dole ne a bi matakan sulhu na siyasa ta hanyar amfani da yarjejeniyar da aka cimma ta birnin Geneva.

Yarjejeniyar mai lamba 2254, ta nemi a gudanar da garambawul a kundin tsarin mulkin kasar, gami da aiwatar da sahihin zabe karkashin kulawar MDD, wanda zai kunshi dukkan bangarorin a'lummar kasar ta Syria ciki har da baiwa 'yan kasar dake zaune a kasashen ketare damar shiga a dama da su. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China