in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani jirgin saman fasinja ya yi sabi zarce a Najeriya
2018-02-21 11:47:13 cri
A jiya ne jirgin saman fasinja na Dana Air a Najeriya, ya dan lalace, bayan da ya wuce titin saukarsa a birnin Fatakwal dake kudancin kasar, koda yake babu wani fasinja da ya ji rauni.

Mai magana da yawun hukumar kula da filayen jiragen sama na Najeriya Henrietta Yakubu ya shaidawa manema labarai cewa, jirgin na Dana Air, yana dauke ne da fasinjoji 49 a lokacin da lamarin ya faru.

Yakubu ya ce, ana zaton ruwan saman da ake shekawa kamar da bakin kwarya gami da iska mai karfi da kuma tsawa ne suka haddasa lamarin. Shi dai jirgin na Dana Air ya taso ne daga Abuja, babban birnin kasar ta Najeriya. Kuma an kwashe dukkan fasinjojin ba tare da wata matsala ba.

Rahotanni na cewa, an rufe titin saukar jiragen na dan wani lokaci, amma daga bisani an sake bude shi bayan da aka duba shi.

Idan za a iya tunawa, a ranar 3 ga watan Yunin shekarar 2012, jirgin saman na Dana Air, ya taba yin hadari a yankin da jama'a ke zaune a birnin Legas, inda dukkan mutane 153 da kuma wasu mutane 40 dake cikin wani bene mai hawa biyu da jirgin ya fada a kansu suka mutu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China