Kwamitin sanya ido da ladaftarwa na jam'iyyar kwaminis mai mulkin kasar(JKS) shi ne ya bayyana hakan jiya Laraba cikin wata sanarwa, yana mai cewa an samu jami'an da tafka manyan kura-kurai, ciki har da rashin aiwatar da shawarar da kwamitin koli na JKS ya yanke yadda ya kamata, gawaza wajen daidaita matsalolin dake da nasaba da kawar da talauci da yin sakaici da aiki.
Sanarwar ta ce, an bukaci Hui Jian, sakataren kwamitin JKS na birnin Zhangjiakou da magajin garin birnin Wu Weidong da su zargi kansu, yayin da aka ja kunnen mataimakin sakataren kwamitin JKS na birnin Liu Baoqi da kuma mataimakin magarin garin birnin Yan Wanglin.
Kimanin jami'ai 11 ne aka samu da laifin keta ka'idojin yaki da talauci a birnin na Zhangjiakou. (Ibrahim)