A shekarar da ta gabata, ma'aunin zaman rayuwa mafi kankanta na mazaunan birane na kasar Sin ya karu da kashi 9.4 bisa dari, da kashi 14.9 bisa dari a kauyuka.
Kuma bisa shirin kasar Sin, nan da shekarar 2020, ana fatan kawar da talauci a kasar baki daya. Mr. Huang ya ce, a nan gaba, za a kara taimakon zaman rayuwa da ake baiwa mazauna kauyuka a dukkan fannoni, da kuma kyautata manufofi da shirye-shiryen a yankunan da ke fama da kangin talauci, da kara tsarin tallafin da ake baiwa yankunan karkara. Za kuma a ci gaba da hada kai da kungiyoyin fararen hula ta yadda za su shiga cikin shirin kawar da talauci a duk fadin kasar. (Maryam)