in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kaddamar da wani sabon shirin yaki da talaucin da rashin lafiya ke haddasawa
2017-12-18 09:07:22 cri

Kasar Sin ta kaddamar da wani shirin yaki da talaucin da rashin lafiya ke haddasawa, a cewar Xia Gengsheng, dan majalisar gudanarwar kasar Sin dake jan ragamar ofishin yaki da talauci da samar da ci gaba na kasar, Shirin da zai kai har cikin watan Fabrairu mai zuwa, na da nufin amfani da lokacin da manoma ke gida bayan kammala girbi da na bikin bazara wato lokacin da 'yan ci rani ke komawa gida, wajen lalubo adadin matalauta dake dauke da cututtuka tare da sanar da su game da sabbin dabarun.

Xia Gengsheng, ya ce a karshen shekarar 2016, sama da kaso 50 na matalauta mazauna larduna 10 na kasar Sin sun tsinci kansu cikin halin talauci ne sanadiyyar rashin lafiya.

Kasar Sin na da niyyar fitar da dukkan al'ummarta daga kangin talauci ta yadda zuwa shekarar 2020, a ko wacce shekara, matsakaicin yawan kudin shigar ko wanen mutumin karkara zai kai yuan 2,300 kwatankwacin dala 348.

Kasar Sin dai, ta dauki kwararan matakan taimakawa marasa lafiya matalauta dake yankunan karkara.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China