in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar 'yan sandan Najeriya ta ce an kashe mutane 18 a harin tagwayen boma bomai
2018-02-18 12:47:31 cri

Hukumar 'yan sandan jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya ta ce mutane 18 ne suka rasu kana wasu 22 kuma suka jikkata a wani harin da aka kaddamar ranar Juma'a a wata kasuwa.

Babban jami'in hukumar 'yan sanda Damian Chukwu, ya tabbatarwa manema labarai faruwar lamarin a Maiduguri, babban birnin jahar Borno, ya ce wani namiji guda da wasu mata biyu 'yan kunar bakin wake ne suka tada boma boman dake jikinsu a kasuwar Kifi dake garin Konduga.

Sai dai jami'in ya ce al'amura sun lafa a yankin bayan faruwar lamarin.

Amma a ta bakin Bashir Garza, jami'in hukumar bada agajin gaggawa ta kasar NEMA dake shiyyar ya ce, adadin mutanen da suka mutu 17 ne, kana wasu 51 kuma sun samu raunuka.

Wani jami'in kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ya ce mutane 22 ne suka mutu, kana wasu 28 kuma suka jikkata a sanadiyyar harin bom din.

Idrissa Bana, wani da ya ganewa idonsa faruwar lamarin ya bayyana cewa, maharan uku sun tada boma boman dake jikinsu ne a lokaci guda, a cikin kasuwar mai cinkoson jama'a.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da harin, sai dai ana zargin mayakan 'yan ta'adda na Boko Haram da kaddamar da hare-haren kunar bakin wake ta hanyar amfani da 'yan mata, don cimma burinsu a shiyyar arewa maso gabashin kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China