in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta tabbatar da sakin malaman jami'a da 'yan sanda mata da Boko Haram ta yi garkuwa da su
2018-02-12 09:07:36 cri

Hukumomin Najeriya sun ba da tabbacin cewa, nan ba da jimawa ba za'a saki malaman jami'ar nan 3 da 'yan sanda mata su 10 wadanda kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram ta yi garkuwa da su a shekarar da ta gabata.

Jami'an 'yan sandan ciki, sun tabbatar da sakin malaman jami'ar tare da 'yan sanda mata, hukumar ta ce, tun a ranar Asabar ta yi wa shugaba Muhammadu Buhari karin haske dangane da matakan da aka bi wajen kubutar da jami'an

A sanarwa da fadar shugaban kasar Muhammadu Buhari ta fitar, ta sake tabbatar da saki jami'an wadanda aka yi garkuwa da su, bayan jerin yarjejeniyoyi da aka cimma da kungiyar wanda hukumar ba da agaji ta Red Cross ta shiga tsakani.

Sanarwar ta ce, an tanadi tawagar likitoci da kwararru a fannin halayyar dan adam don ba su kulawa ta musamman.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China