in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An hallaka mutane 6 yayin harin Boko Haram a arewa mai nisa na Kamaru
2018-02-06 10:17:11 cri

A kalla fararen hula 6 ne mayakan kungiyar Boko Haram suka hallaka a dare ranar Lahadi, a yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru.

Mahukuntan yankin sun bayyana cewa, mayakan kungiyar sun farwa al'ummar Mayo-Tsanaga, inda suka hallaka maza 5 da wata mace mai juna biyu guda.

Kaza lika maharan sun kona gidaje da majami'u yayin harin na kimanin sa'a guda. To sai dai kuma rahotanni sun tabbatar da cewa, dakarun gwamnatin kasar sun kaiwa mazauna yankin dauki.

Yankin arewa mai nisa na kasar Kamaru dai na iyaka da yankin da kungiyar Boko Haram ke da karfi a arewa maso gabashin tarayyar Najeriya. A watan Janairun da ya shude kadai, mutane 26 sun rasa rayukan su sakamakon hare hare 30 da kungiyar Boko Haram ta kaddamar a yankin na arewa mai nisa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China