in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata kotu a Najeriya ta yankewa mutumin da ya yi garkuwa da 'Yan matan Chibok hukuncin shekaru 15 a gidan yari
2018-02-14 09:15:31 cri

Wata kotu a tarayyar Najeriya ta yanke wa Haruna Yahaya, mutumin da ya yi garkuwa da 'yan matan sakandaren garin Chibok 276 a yankin arewa masu gabashin kasar shekaru 4 da suka gabata, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 15.

A ranar Litinin din da ta gabata ce dai kotun ta gurfanar da Haruna Yahaya mai shekaru 35 kana tsohon 'ya'yan kungiyar Boko Haram bisa tuhumarsa da aikata laifukan ta'addanci da kuma yin garkuwa da mutane.

Yahaya wanda ke tsare tun cikin shekarar 2005, yana daga cikin 'yan ta'addan Boko Haram 1,000 da suke fuskantar shari'a a Najeriya.

Ya kuma fadawa kotun cewa, ya shiga kungiyar ce a shekarar 2014, kuma yana daga cikin wadanda suka yi garkuwa da 'yan matan na Chibok a ranar 14 ga watan Afrikun shekarar 2014.

Haruna Yahaya dai ya amsa laifuka biyun da ake tuhumarsa da aikatawa.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China