Sabon jirgin kasa mai matukar saurin tafiya mai suna "Fuxing" a yau Litinin ya fara zirga zirga tsakanin biranen Beijing da Shanghai.
Da misalin karfe 11:05 na safiyar yau Litinin jirgin samfurin CR400AF ya tashi daga tashar jirgin kasa ta kudu a birnin Beijing zuwa birnin Shanghai. Kuma a makamancin wannan lokaci jirgin samfurin CR400BF ya baro tashar jirgin kasa ta Shanghai Hongqiao zuwa Beijing.
Sabon jirgin kasan mai tsananin gudu, wanda ke amfani da lantarki mai karfin gaske, wato electric multiple units (EMU) a turance, yana iya gudun kilomita 400 cikin ko wace sa'a, kuma ya kan gudu da kilomita 350 a ko wace sa'a.
Wannan jirgin, an tsara shi da kuma kera shi ne a kasar Sin.(Ahmad Fagam)