in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tabbas ne dankon zumuncin dake tsakanin kasashen Sin da Afirka zai karu, in ji ministan harkokin wajen Sin
2018-01-17 14:11:55 cri

Jiya Talata 16 ga wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya amsa tambayoyin manema labaru dangane da ziyararsa a kasashe 4 na Afirka.

Mista Wang ya bayyana cewa, duk da irin bunkasuwar da kasar Sin ta samu, ta mayar da kanta a matsayin wata kasa mai tasowa. Kasashen Sin da Afirka suna kasancewa kamar aminai ne wadanda suka amince da juna da yin hadin gwiwa a tsakanin juna cikin sahihanci ta fuskar tattalin arziki, musamman ma siyasa. Wadannan kasashe 4 na Afirka da ya ziyarta a wannan karo sun sha bamban da juna, amma akwai abubuwan bai daya da suke da su. Da farko, babban taron wakilan JKS karo 19 ya ci gaba da yin tasiri a kasashen duniya, musamman ma a kasashen Afirka masu tasowa. Na biyu, kasashen Afirka suna fatan raya tattalin arziki ta hanyoyi daban daban. Na uku, kasashen Afirka suna zumudin ingantan hadin gwiwa a tsakaninsu da kasar ta Sin.

Wang Yi ya imani da cewa, sakamakon kokarin da kasashen Sin da Afirka suke bayarwa, ya sa tabbas ne taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka a bana zai zama wani kasaitaccen taro ne na daban, kana dankon zumuncin dake tsakanin kasashen Sin da Afirka zai karu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China