Jami'an da suka bayyana haka yayin wani taron tattaunawa kan inganta zuba jari, a wani bangare na baje kolin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Afrika don bunkasa masana'antu dake gudana a birnin Nairobi, sun ce za a iya amfani da jari da kwarewar kasar Sin wajen samar da ingantattun cibiyoyin masana'antu a nahiya mafi girma ta biyu a duniya.
Jagoran ayarin masu inganta zuba jari na hukumar kula da harkokin zuba jari ta kasar Habasha Aschalew Tadesse, ya ce a daidai lokacin da kasashen Afrika ke yunkurin farfado da bangaren masana'antu, kasar Sin na da muhimmiyar rawar da za ta taka.
A nasa bangaren, shugaban cibiyar harkokin cinikayya tsakanin kasa da kasa a yankin Asiya da Fasifik Jiang Xuejun, kira ya yi ga kasashen Afrika su samar da kyawawan sharudan da za su saukakawa kasar Sin wajen zuba jari a bangaren masana'antun.
A nasa bangaren, jami'in inganta zuba jari na hukumar raya kasa ta Zambia Chisanga Pule, cewa ya yi fasahohi da jarin kasar Sin za su zama jigon lalubo damammakin da nahiyar ke da su a bangarori kamar na hakar ma'adinai da sarrafa kayayakin gona da fasahar zamani. (Fa'iza)