in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta gama da Boko Haram
2018-02-05 09:33:16 cri

Jagoran rundunar sojojin Najeriya dake yaki da kungiyar Boko Haram a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar Manjo Janar Rogers Nicholas, ya ce sun kammala murkushe mayakan kungiyar, tare da fatattakar su daga maboyar su dake dajin Sambisa.

Nicholas, wanda ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a ranar Asabar, yayin taron kaddamar da rundunar hadin gwiwa ta dakarun Najeriya da Kamaru a birnin Maiduguri, ya ce hadin kan sassan biyu ya haifar da gagarumar nasara a yakin da suke yi da masu tada kayar baya.

Ya ce, dakarun dake aiki karkashin shirin "DEEP PUNCH II" sun kame yankin nan na "Camp Zairo," dake dajin Sambisa mai matukar tasiri ga kungiyar Boko Haram, matakin da ya tilastawa daruruwan mayakan kungiyar mika wuya, yayin da wasu da dama suka tsere, baya ga sama da fararen hula 100 da aka ceto.

Jami'in ya ce, kame sassan dajin Sambisa da sojojin suka yi, ya karya kashin bayan magoya bayan Abubakar Shekau. Daga nan sai ya yi kira ga mayakan Boko Haram da suka tsere su mika wuya ga jami'an tsaro, yana mai cewa, ba za a hallaka su ba muddin suka ajiye makaman su.

A daya hannun kuma Nicholas ya ce, rundunar sa za ta tara bayanai na fararen hula da aka ceto daga kungiyar, sa'an nan a shigar da su shirin sauya tunani da mayar da su cikin al'umma.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China