in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Libya ta dauki matakan tabbatar da tsaro don dakile hare haren ta'addanci a Benghazi
2018-02-12 11:48:20 cri

Gwamnatin kasar Libya dake da ofishinta a gabashin kasar ta bayyana cewa, ta dauki wasu matakan tsaro domin dakile barazanar hare haren ta'addanci a gabashin birnin Benghazi.

Gwamnatin rikon kwaryar ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, majalisar ministoci da shugabannin tsaro na birnin Benghazi, sun dauki matakan tsaurara tsaro domin magance barazanar harin ta'addanci bayan wani taron gaggawa da suka gudanar tare da firaministan kasar, Abdullah Thanni.

Sanarwar ta ce, nasarorin dakarun tsaron kasar da dakarun sojin dake mara musu baya za su iya yin tasiri a birnin na Benghazi ne kadai idan aka samun nasarar aikin tabbatar da tsaron. Abokan gaba suna amfani da hanyoyi na kunar bakin wake domin wargaza yanayin tsaro a birnin.

Tuni dai gwamnatin kasar ta ba da umarnin kakkafa kyamarorin aikin tsaro a masallatan birnin, inda kuma aka sada su kai tsaye da babbar cibiyar tsaro ta ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China