in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta jadadda kudurinta na ganin tsarin siyasar Libya ya cimma nasara
2018-02-18 12:29:36 cri
Shirin wanzar da zaman lafiya na MDD dake Libya UNSMIL, ya jaddada kudurinsa na aiki wajen ganin tsarin siyasar kasar ya cimma nasara.

Cikin sakon da aka fitar a ranar da ake cika shekaru 7 da hambarar da mulkin Gaddafi, shirin ya sabunta kudurinsa na aiki da kowa a fadin kasar, don kyautata tsarin siyasa da kawo karshen sauye-sauyen gwamnati tare da bude wani babi mai cike da tabbas bisa amfani da kundin tsarin mulki da ya kunshi sahihin zabe da cimma sulhu a kasar.

Shirin ya ce yayin da aka shiga shekara ta 7 bayan hambarar da mulki a kasar a ranar 17 ga watan Fabreru, yana tunawa da irin sadaukarwar da al'ummar kasar suka yi na ganin sun rayu cikin daraja da kima.

Tun cikin watan Satumban da ya gabata ne shirin ya fara daukar nauyin tattaunawar cimma matsayar sake fasalin yarjejeniyar siyasa tsakanin jam'iyyun kasar, da nufin kawo karshen rikicin siyasar da ake fuskanta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China