in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi Allah wadai da harin da aka kaddamar a wani masallaci a Benghazi na kasar Libya
2018-02-10 13:10:24 cri
Hukumar tallafawa shirin wanzar da zaman lafiya ta MDD a kasar Libya (UNSMIL) ta yi Allah wadai da harin bom da aka kaddamar a wani masallaci dake birnin Benghazi, na arewacin kasar Libya, inda ya hallaka mutane 2 da kuma jikkata mutane 143 cikinsu har da kananan yara.

A sanarwar da ta fitar, UNSMIL, ta yi Allah wadai da kakkausar murya dangane da wannan kisan rashin imani a yankin alMajouri dake Benghazi, wanda shi ne hari na biyu mafi girma da aka kaddamar a wurin bauta a birnin Benghazi a kasa da wata guda. Rahotanni game da adadin fararen hular da aka raunata a harin abin ta da hankali ne.

Hukumar MDDr ta ce, kaddamar da hare hare kan fararen hula haramtaccen laifi ne a karkashin dokokin kasa da kasa, kuma tamkar aikata laifukan yaki ne, inda ta bukaci a gudanar da bincike bisa adalci don hukunta wadanda ke da hannu wajen aikata laifukan.

Ita ma gwamnatin Libya dake samun goyon bayan MDDr dake Tripoli, ta yi Allah wadai da harin bom din, inda ta lashi takobin cigaba da yakar ayyukan ta'addanci da masu barazanar wargaza zaman lafiya da tsaron kasar, kana da gurfanar da wadanda ke da hannu a gaban shari'a.

Libya ta tsunduma cikin tashin hankali da rikicin siyasa ne, tun bayan kifar da gwamnatin shugaban kasar Muammar Gaddafi a shekarar 2011.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China