Hua ta bayyana haka ne a yayin da take amsa tambayoyin manema labaru game da ra'ayin kasar Sin kan cimma wannan yarjejeniya, inda ta bayyana cewa, kasar Sin tana goyon bayan yunkurin tattaunawar siyasa na Libya karkashin shugabancin MDD, tana kuma maraba da cimma wannan yarjejeniyar siyasa da rukunonin kasar suka yi a kasar Morocco. Ta kuma yi kira ga bangarorin da su ci gaba da sulhuntawa ta hanyar yin shawarwari, da nufin farfado da zaman lafiya a kasar, wannan mataki ya dace da moriyar jama'ar kasar, kana zai taimaka wajen tabbatar da tsaro, zaman lafiya da kuma bunkasuwar yankin. (Bilkisu)