Yaran kasar Ghana sun bukaci gwamnatin kasar da ta aiwatar da tsare tsaren ba su kariya yadda ya kamata, domin kaucewa hana su samu ingantacciyar rayuwa, da kuma hana duk wani abu da zai iya hana su samu damar shiga makarantu a kasar.
A matsayin wani bangare na bikin murnar ranar yaran Afrika, cibiyar tattara bayanai ta MDD (UNIC), tare da hadin gwiwar gidauniyar Abibiman Foundation, wata hukuma mai zaman kanta ne suka shirya bikin, inda suka gayyaci yara 'yan makaranta 20 'yan tsakanin shekaru 12-16 don su halarci bikin.
Domin gudanar bikin tunawa da wannan ranar, wadda ta fado a ranar 16 ga watan Yuni, yaran sun bukaci gwamnati da ta hukunta dukkan wadanda aka samu da laifin bautar da kananan yara domin ya zama darasi ga 'yan baya.
Ana gudanar da bikin ranar yaran Afrika, domin tunawa da wasu yara 'yan makaranta sama da guda 100 wadanda aka hallaka a zamanin gwagwarmayar yaki da nuna wariyar launin fata a Afrika ta kudu a Soweto a watan Yunin shekarar 1976, inda ake ci gaba da fafutukar nema musu 'yancin ba su ilmi mai inganci.
Kungiyar tarayyar Afrika (AU), wacce a baya aka kira (OAU) a shekarar 1990, ita ce ta kebe wannan rana domin gwagwarmayar nemawa yaran Afrika ingantacciyar rayuwa.(Ahmad Fagam)