in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF ta yiwa miliyoyin yara a Najeriya alkuran riga kafi
2017-01-27 13:20:54 cri
Asusun tallafawa kananan yara na MDD UNICEF ya bayyana cewa ya yiwa miliyoyin yara a jihohi uku da rikicin Boko Haram ya fi shafa alluran rigakafi, a daidai lokacin da asusun ke kammala aikinsa na rigakafi a kasar.

Kakakin MDD Stephane Dujarric ya shaidawa manema labarai cewa, shirin rigakafin wani bangare ne na magance barkewa cututtuka a yankin arewa maso gabashin kasar ta Najeriya. A cewar Dujarric shirin ya kunshi gyara cibiyoyin kiwon lafiya da kafa na wucin domin taimakawa mata da kananan yara da kuma magance barkewar cututtukan yau da kullum.

Kakakin na MDD ya shaidawa taron manema labarai cewa, yayin babban shirin riga kafin da za a kammala a wannan makon, ana fatan yiwa yara miliyan 4.7 rigakafi sakamakon bullar cutar kyanda a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Shirin rgakafin da zai hada jihohin Adamawa da Borno da Yobe da rikicin Boko Haram ya shafa, inda matsalar tsaro ta hana gudanar da shirin riga kafi.

Kimanin cututtukam kyanda 25,000 aka bada rahoton bullarsu tsakanin yara a Najeriya a shekarar 2016, kuma kashi 97 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar yara ne 'yan kasa da shekaru 10, kana wasu yara a kalla 100 sun mutu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China