Sabon hasashen da aka fitar yayin wani taron tattaunawa kan kawo karshen auren wuri da ya gudana jiya Litinin a Dakar babban birnin Senegal, na da nufin fiddo da yankunan da 'yan mata suka fi fuskantar barazanar auren wuri a duniya.
A cewar UNICEF, yayin da yawan auren wuri a yankunan yammaci da tsakiyar Afrika ya ragu cikin shekaru 20 da suka gabata, har yanzu da sauran rina a kaba, domin a cikin kowanne mata 10, akan yi wa hudu aure kafin su cika shekaru 18, sannan akan yi wa 1 daga cikin 3 aure kafin ta kai shekaru 15.
Yammaci da tsakiyar Afrika sun kushi kasashe 6 daga cikin 10 da aka fi samun yawan auren wuri a duniya, inda suka hada da Niger da Jamhuriyar Afrika ta tsakiya da Chadi da Mali da Burkina Faso da Guinea.
A cewar Bankin Duniya, dabi'ar na bukatar yunkurin kasashen duniya wajen rage talauci da karuwar jama'a, al'amarin dake da mummunan tasiri kan ci gaban ilimi da lafiyar mata da yara. (Fa'iza Mustapha)