Karuwar adadin ba zai rasa nasaba da irin sabbin dabarun da mayaka 'yan tada kayar baya ke amfani dasu ba: kawo yanzu, yara 117 ne aka yi amfani dasu wajen kaddamar da hare haren kunar bakin wake a wuraren taruwar jama'a a kasashen Najeriya, Nijer, Kamaru da Chadi, tun daga shekarar 2014.
Rahoton ya kara da cewa an fi yin amfani da yara mata wajen kitsa wadannan hare haren.
Sakamakon faruwar wadannan matsaloli, yara mata da maza, har ma da jarirai sun kasance a matsayin wata barazana a duk lokacin da aka ga suna kaiwa da kawowa a wuraren taruwar jama'a, kasuwanni da wuraren binciken ababan hawa.
Rahoton ya kuma zayyana wasu daga irin kalubalolin da kananan hukumomi ke fuskanta saboda karuwar irin wadannan yara, wadanda sau da dama ake rike dasu na tsawon lokaci domin yi musu tambayoyi.
A shekarar 2016, kananan yara 1,500 ne suke karkashin kulawar kananan hukumomin a kasashe hudu.