in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron kolin Afrika kan albarkatun man fetur mafi girma a Najeriya
2018-02-20 12:22:03 cri

A ranar Litinin aka bude taron koli game da albarkatun man fetur na Afrika a Abuja, hedkwatar mulkin Najeriya, wanda shi ne irinsa na farko mafi girma, da nufin nazartar yadda za'a farfado da kamfanonin mai a Afrika.

Ministan albarkatun man fetur na Najeriya Ibe Kachikwu, shi ne ya jagoranci bude taron a madadin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa Najeriya a shirye take ta samar da jagoranci a fannin albarkatun mai da iskar gas a nahiyar Afrika.

Kachikwu ya ce, an shirya taron kolin kasa da kasa kan albarkatun man fetur ne domin ya kasance a matsayin wani dandali mafi muhimmanci wanda zai hada Afrika da sauran sassan duniya.

Taron kolin zai baje-kolin irin sabbin fasahohin zamani da ake amfani da su a harkokin albarkatun man fetur, da kayayyakin da ake amfani da su, da kuma irin damammakin da ake da su ta fannin zuba jarin kamfanonin hakar mai da iskar gas na duniya.

Kachikwu ya ce, taron zai ba da damar samun cin moriya ta fuskar tattalin arziki, da samar da guraben ayyukan yi, da kuma fadada harkokin cinikayya a Najeriya da ma Afrika baki daya.

Masana'antar sarrafa man fetur ta Najeriya ita ce mafi girma a Afrika inda aka yi amana yana iya adana gangar danyen mai biliyan 37 da iskar gas cubic triliyan 192.

Daruruwan wakilai daga kamfanonin mai na kasashen duniya daban daban ne ke halartar taron na kwanaki 5 a Abuja.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China