in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamfanonin Sin za su yi aikin shimfida bututan mai a tekun Najeriya
2018-01-14 12:48:40 cri

Wasu manyan kamfanonin kasar Sin biyu sun gudanar da bikin kaddamar da fara aikin shimfida bututan mai a cikin teku na aikin kamfanin matatar man fetur ta Dangote a birnin Lagos, cibiyar kasuwancin Najeriya.

Manyan jami'an rukunin kamfanonin Dangote a Najeriya, da Xie Xianju, mataimakin janar manajan kamfanin China Harbor Engineering Co dake (Nigeria) da Zhang Qing, janar manajan kamfanin China Offshore Oil Engineering Company (COOEC) sun halarci bikin kaddamar da aikin, a kusa da yankin kasuwanci marar shinge dake Lekki a birnin Lagos.

Aikin ya kunshi na shimfida bututan mai, da na iskar gas, da na takin zamani, da na sarrafa man fetur, da na tace mai na kamfanin Dangote wanda zai lashe tsabar kudi dalar Amurka biliyan 17.

Shi dai aikin ya hada da shimfida bututan man guda 9 a karkashin teku mai tazarar kilomita 100 a cikin teku mai zurfin mita 40, da na shimfida bututan mai 6 mai tsawon inci 24 da kuma guda 3 mai tsawon inci 48.

Xie ya bayyana cewa, ingancin aikin da za su gudanar zai kasance mafi daraja a duniya, ya kara da cewa, kamfaninsu zai tattara dukkan kwarewar da yake da ita wajen gudanar da aikin.

Sumil Katawia na rukunin kamfanonin Dangote ya bayyana cewa, burin da suke da shi na samun aikin shimfida bututan mai mafi inganci ne ya sanya suka gayyaci kamfanonin na COOEC da China Harbor don gudanar da aikin.

Aikin matatar man na Dangote wanda ake gudanar da shi a halin yanzu, zai ragewa Najeriya hasarar dala biliyan 12 da kasar ke yi a duk shekara wajen shigo da tacaccen mai daga waje, kana zai samar da ayyukan yi na kai tsaye kimanin 4,000 kuma zai rage tsadar farashin man fetur a Najeriyar.

Haka zalika, aikin zai bunkasa cigaban tattalin arzikin Najeriya sakamakon guraben ayyuka da samar kimanin 145,000.

Ana sa ran za a kaddamar da aikin tace gangar danyen mai 650,000 a ko wace rana daga watan Satumbar shekarar 2019, in ji jami'an kamfanin.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China