Karamin ministan ma'aikatar mai a tarayyar Najeriya Ibe Kachikwu, ya sanar da dakatar da aikin binciken albarkatun mai da ake yi a yankin tafkin Chadi, bayan da mayakan Boko Haram suka kaiwa jami'an dake aiki a wurin wani kazamin hari.
Ministan ya ce, gwamnati ta yanke shawarar tsayar da aikin, har lokacin da za a samu cikakken yanayi na tsaro, wanda zai ba da damar ci gaba da aiki ba tare da wata fargaba ba.
Mr. Kachikwu ya ce, kafin fara aikin, sai da kamfanin sarrafa albarkatun mai na Najeriya NNPC ya samu cikakken rahoton tsaro daga rundunar sojin kasar, sai dai kuma lamarin da ya auku ya sanya dole a dakatar da aikin zuwa wani lokaci.
Wasu kafafen watsa labarai na cikin gida sun bayyana cewa, sojojin kasar 18 da wasu direbobin kamfanin na NNPC su 4 sun gamu da ajalin su, yayin dauki ba dadin da aka yi da mayakan na Boko Haram. Har wa yau fafatawar ta sabbaba rasuwar fararen hula a kalla 20.(Saminu)