in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya ta musanta mai da tsohuwar Ministar mai ta kasar gida domin fuskantar Shari'a
2017-10-05 12:25:47 cri
Ministan Shari'a na Nijeriya Abubakar Malami, ya ce Gwamnatin kasar ba ta da wani shiri a yanzu, na mai da tsohuwar ministar man kasar Deziani Allison-Madueke gida domin fuskantar shari'a.

Allison-Madueke da ake bincikenta a Birtaniya, ta bukaci Gwamnatin Nijeriya ta mai da ta gida don fuskantar tuhume-tuhumen cin hanci da ake mata.

Abubakar Malami ya shaidawa manema labarai jiya a Abuja fadar mulkin kasar cewa, mai da Allison Madueke zai kawo tsaiko ga binciken da ake mata a Birtaniya.

Ya ce hukumomin Birtaniya sun dauki matakai kan ayyukan cin hanci da ya shafi 'yan Nijeriya.

Ministan ya ce Nijeriyar na daukar matakai da dama na yaki da cin hanci a ciki da wajen kasar.

Ya ce akwai fahimta tsakanin Nijeriya da wasu kasashe, musammam Birtaniya wajen dawo da dukiyar kasar da aka yi sama da fadi da su.

Allison Madueke na fuskantar tuhume-tuhume kan halasta kudin haram da mallakar kadarori a Birtaniya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China