in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tsagerun Neja Delta a Nijeriya sun nemi matasan yankin arewacin kasar su fice daga yankinsu mai arzikin mai
2017-06-17 11:29:55 cri
Kawancen kungiyoyin tsagerun yankin Neja Delta mai arzikin man fetur a Nijeriya, sun ba 'yan arewacin kasar dake zaune a yankin wa'adin ficewa.

Kungiyoyin sun bada wa'adin ne bayan sun gudanar da wani taro a ranar Alhamis.

Jaridar The Guardian ta kasar, ta ruwaito a jiya Jumma'a cewa, tsagerun sun yi barazanar lalata rijiyoyin mai mallakar 'yan arewa kafin ranar 1 ga watan Oktoba.

Wa'adin dai martini ne ga makamacinsa da wasu matasan yankin arewacin kasar suka ba 'yan yankin kudu.

Amma wani mai sharhi kan al'amura ya ce barazanar da tsagerun na Neja Delta suka yi na rufe yankin, ka iya kawo matsala ga aikin samar da man fetur da kudin shiga ga kasar.

A ranar Talata da ta gabata ne Mukaddashin Shugaban kasar Yemi Osinbajo, ya fara tuntubar shugabanni a fadin kasar domin samar da zaman lafiya da zai dakatar da matasan daga ci gaba da yin barazanar.

Tsagerun na Neja-Delta sun zargi gwamnati da jami'an 'yan sanda da rashin daukar matakan da suka kamata na kawo karshen rikicin na kabilanci, suna masu bukatar gwamnati ta mai da rijiyoyin mai mallakar 'yan arewa ga al'ummar yankin Neja Delta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China