in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
FAO zai taimakawa Afirka ta inganta karfinta na tagwaita irin amfanin gona
2016-10-28 10:27:58 cri
Shirin samar da abinci da aikin gona na MDD, wato FAO, ya bayyana shirin sa na taimakawa kasashen nahiyar Afirka ta yadda za su inganta karfi da kwarewarsu na tagwaita iri amfanin gona.

Shugaban kungiyar hukumomin kula da ingancin amfanin gonan da ake tagwaita na Afirka(ANABAA) Dr. Willy Tonui shi ne ya bayyana hakan yayin zantawarsu da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin a birnin Nairobin kasar Kenya. Yana mai cewa, shirin na FAO zai tattauna da kasashen Afirka game da matakan tagwaita irin amfanin gona, a wani mataki na kara ingancin abinci a nahiyar.

Yanzu haka dai, kasashen Burkina Faso, da Sudan,da Sudan ta kudu sun fara sayar da nau'o'in abincin da aka tagwaita, yayin da wasu kasashen nahiyar da dama suka fara gwajin tagwaita irin amfanin gona.

Shirin na FAO dai zai fara kaddamar da wannan shiri ne a kasashen gabashin Afirka, daga bisani kuma a kaddamar da shi a sauran kasashen nahiyar. Su ma hukumomin kula da ingancin abincin da aka tagwaita za su sa-ido wajen hade dokokin da abin shafa a fadin shiyyar.

Wannan yana nufin cewa,duk kasar da ta amince da wani nau'in abincin da aka tagwaita, wajibi ne dukkan kasashen nahiyar su amince da shi.

Masana na cewa, wannan mataki zai taimaka wajen bunkasa harkokin cinikayya tsakanin kasashen Afirka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China