in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tallafin da kasar Sin ta baiwa Afirka a fannin tsaron abinci ya yi tasiri
2015-10-01 13:57:11 cri
Jami'in hukumar samar da abinci da aikin gona ta MDD ko FAO a takaice, Sourakata Bangoura, ya bayyana cewa, sakamakon huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka, irin taimakon da take baiwa Afirka a fannin tsaron abinci ya taimakawa al'ummar nahiyar matuka.

Sourakata Bangoura, jami'in shiyya na hukumar ta FAO reshen Afirka da ke birnin Accra na kasar Ghana, ya bayyana cewa kasar Sin muhimmiyar kasa ce da ke taimawa ayyukan FAO matuka.

A watan Yuni ne kasar Sin da FAO suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar dala miliyan 50 domin tallafawa kasashe masu tasowa inganta tsare-tsarensu na samar da cimaka cikin dogon lokaci da kuma inganta dabarun noma.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi alkawarin samar da dala biliya biyu domin tallafawa dangantakar kasashe masu tasowa ta kudu da kudu da kuma kasashe masu tasowa wajen yakar talauci Afirka da kasashen da ke Latin Amurka da kasashen Asiya za su amfana da dukkan taimakon da kasar Sin ta bayar.

Tun kafuwar shirin dangantaka tsakanin kasashe masu tasowa a shekarar 1996, kasar Sin na daya daga cikin manyan masu ruwa da tsaki dake tallafawa Afrika da sauran kasashe masu tasowa wajen samar da horo, taimakawa ci gaban masana'antu da kuma fasahohi. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China