in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar FAO ta yi kashedi game da yiwuwar karancin abinci a kudancin Afirka
2015-12-24 10:33:53 cri
Hukumar samar da abinci da ayyukan gona ta majalissar dinkin duniya wato FAO, ta yi kashedi game da yiwuwar gamuwa da karancin abinci, da albarkatun dabbobi a yankuna kudancin Afirka, sakamakon matsalar karin dumamar yanayi ko El Nino a turance.

Cikin wani rahoto da hukumar ta fitar a jiya Laraba, ta ce mai yiwuwa ne a samu karancin amfani a kakar dake tafe, matakin da tuni ya haifar da karuwar farashin abinci, yake kuma matsin lamba ga shirin tsirin hatsi na 2016.

Kasashen da FAOn ta lasafta a matsayin wadanda ka iya fuskantar wannan matsala sun hada da Afirka ta kudu, da Habasha, da Lesotho da Swaziland da dai sauran su.

Rahoton ya kara da cewa, matsakaitan manoma dake wannan yanki na dogaro ne da noman damuna, wanda karancin ruwa a wannan lokaci ke haifar musu da gagarumar matsala.

Yanayin dumamar yanayi na El Nino a wannan karo ya dara irin wanda aka gani cikin shekaru 18 da suka gabata, inda ake hasashen tsanantar sa a farko shekarar 2016, gabanin fara girbin amfanin gona a sassan kasar Afirka ta kudu.

Hasashen yanayi ya nuna cewa, mai yiwuwa ne a ci gaba da fuskantar karancin ruwan sama tsakanin watannin Disamba da Maris, a mafiya yawan kasashen yankin na kudancin Afirka.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China