in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumar FAO za ta tallafawa tsibiran Afirka da dabarun kandagarkin sauyin yanayi
2016-11-18 11:49:25 cri

Hukumar abinci da raya aikin gona ta MDD FAO, ta sha alwashin tallafawa wasu kasashen Afirka 6 da dabarun inganta noma, wanda ke iya jurewa tasirin sauyin yanayi, a wani mataki na bunkasa tattalin arzikin su.

FAO dai ta yi la'akari ne da muhimmancin dake akwai, na taimakawa wadannan kasashe dake tsuburai, duba da irin matsi da suke fuskanta ta bangaren tasirin sauyin yanayi. Tsibiran dai su ne Cabo Verde, da Comoros, da Guinea-Bissau, da Mauritius, da Sao Tome da Principe, da kuma Seychelles.

An kebe kudi da yawan su ya kai dalar Amurka miliyan 1.5, domin gudanar da wannan aiki na musamman, karkashi asusun tallafawa Afirka, wanda kuma ayyukan sa za su fi bada karfi ga aiwatar da matakan dakile tasirin sauyin yanayi, tare da inganta harkokin noma da cinikayyar amfanin gona.

Har wa yau shirin zai fadada ikon kasashen, wajen kyautata tsare tsaren noma daga gonaki zuwa manufofin gwamnati, matakin da ake fata zai taimaka wajen kauda matsalar karancin abinci mai gina jiki, ya kuma rage kamfar abincin baki daya.

An dai cimma yarjejeniyar aiwatar da wannan kuduri ne a yayin da ake ci gaba da taron sauyin yanayi na COP22 a birnin Marrakesh na kasar Morocco.

Taron MDD na bana dake gudana a Morocco, na da nufin bullo da hanyoyin aiwatar da yarjejeniyar birnin Faris. Cikin muhimman sassan hadda bullo da dabarun kandagarki ga mummunan tasirin da sauyin yanayi ke haifarwa a fannonin aikin gona, da kuma samar da ruwan sha mai nagarta.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China