Rahoton ya ce, kasar Sin ta yi nasarar kafa daya daga cikin cibiyoyin dake hade bankuna mafi girma a duniya. Haka kuma kudaden da ake biya wajen mallakar asusun ajiya a kasar ya yi daidai da na sauran kasashen dake kungiyar G20.
Rahoton ya kara da cewa, a 'yan shekarun nan, mahukuntan kasar ta Sin sun dauki kwararan matakai na yiwa kafar hada-hadar kudaden kasar gyaran fuska ta yadda zai dace da zamani. A hannu guda kuma mahakuntan kasar na bullo da managartan manufofin hada-hadar kudi, da fadada bangaren hada-hadar kudi zuwa yankunan karkarar kasar, da kafa sabbin kafofin samar da hidimomin kudi.
Rahoton ya ce, tsarin Fintech, zai ci gaba da taka rawa wajen bunkasa bangaren hada-hadar kudi na zamani ta hanyar biyan sabbin bukatun jama'a a fannin samar da hidima da kayayyaki. Sai dai rahoton ya kammala da cewa, kasar Sin za ta fuskanci kalubale wajen cimma nasara na dogon lokaci a wannan fanni, yayin da ake kokarin samun ci gaba mai dorewa da yadda ake sakarwa kasuwa mara.(Ibrahim Yaya)