in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hukumomin tsaron kudi na kasar Sin sun dauki tsauraran matakan ladaftarwa
2017-12-28 10:58:12 cri
Wasu alkaluma sun nuna cewa, hukumomin tsaron sha'anin kudade na kasar Sin sun dauki tsauraran matakai kan wadanda suka saba dokokin tafiyar da harkokin kudade a kasar cikin wannan shekara, inda suka samu adadi mai yawa na laifukan da suka shafi sha'anin kudade.

A wata sanarwar da hukumar sanya ido kan yadda ake cinikin takardun hannun jari ta kasar Sin CSRC ta fitar, ya nuna cewa, tun a farkon wannan shekara, hukumar ta CSRC ta samu nasarar gano wasu laifuka da suka shafi ta'ammali da kudi kimanin 224.

Baki daya adadin laifukan da hukumar ta bankado sun kai kashi 74.74 bisa 100 wanda ya kai yuan biliyan 7.48, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 1.14.

Matakin da hukumar ta dauka ya samar da daidaito, da kare muradun masu zuba jari, kana matakin ya kara tabbatar da gudanuwar al'amurra a kasuwannin hada hadar kudade.

Sanarwar ta kara da cewa, an zartas da hukunci kan laifukan da dama da aka aikata, ciki har da laifukan da suka shafi yada bayanan sirri, da yin zamba a harkokin kasuwanci, da masu sojan gona a harkokin kasuwanci. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China