Rahotanni daga kasar Sin na cewa, yawan takardun cacar mai rabo ka dauka da aka sayar domin taimakawa masu bukata a kasar a shekarar 2017 da ta gabata, ya kai Yuan biliyan 217, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 33, wato karuwar kaso 5.1 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gaba ce ta.
Wata sanarwa da cibiyar kula da rarraba takardun cacar mai rabo ka daukar, ta bayyana cewa, a shekarar da ta gabatan an tara sama da Yuan bilyan 62 wajen sayar da irin wadannan takardun cacar mai rabo ka dauka.
Tun a shekarar 1987 ne, aka umarci cibiyar dake karkashin kulawar ma'aikatar tsaron jama'a da ta tattara kudade ta hanyar sayar da takardun cacar mai rabo ka dauka domin taimakawa masu bukata.
Daga shekarar 1987 zuwa 2017 da ta gabata, an sayar da irin wadannan takardun cacar mai rabo ka dauka da suka haura Yuan Tiriluyan 1.8, inda aka tara tsabar kudi har yuan biliyan 537 domin taimaka masu bukata, kamar yadda alkaluman cibiyar suka nuna.
Bisa dokokin da aka tsara, rabin kudaden zai shiga aljihun gwamnati ne, kuma ana amfani da wadannan kudade ne wajen taimakawa ayyukan tsaron jama'a da na jin kai na musamman. Kana ragowar kudaden ana amfani da su wajen taimakawa masu bukata da ayyukan agaji dake karkashin kananan hukumomi. (Ibrahim)