Hakan dai na nufin za a mayar wa kamfanonin da abun ya shafa dukkanin irin wannan haraji da aka karba daga gare su a shekarar ta 2017. Bayanin hakan dai na zuwa ne a gabar da mahukuntan kasar ke daukar karin matakan jawo hankulan masu zuba jari, bayan da wasu kasashe da dama suka fara daukar makamantan wadannan matakai na jawo jarin waje.
Ma'aikatar kudin kasar ta Sin ta bayyana cewa, kamfanonin waje na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar Sin, tare da fadada ci gaban fasahohin masana'antu.
Kaza lika tsarin zai baiwa kamfanonin na waje damar samun riba mai tsoka, ta hanyar karfafa musu gwiwar fadada zuba jari a Sin, matakin da kuma zai haifar da moriya ga sassan biyu.
To sai dai kuma ma'aikatar ta ce dole ne kamfanonin wajen su cika wasu jerin sharudda kafin su samu damar cin wannan gajiya, ciki hadda shiga fannonin da gwamnatin kasar ta Sin ke baiwa fifiko, kana ya kasance suna mayar da ribar da suka ci kai tsaye, ga asusun kamfanonin da ke sarrafa jarin nasu. (Saminu Hassan)