Sanarwar da ma'aikatar ta fitar, ta ce bisa tsarin da zai fara aiki a wata mai zuwa, matsakaicin kudin haraji kan wasu kayayyakin abinci da na lafiya da magunguna da sinadaran da ake amfani da su yau da kullum da takalma da sauran wasu kayayyaki zai sauka zuwa kashi 7.7 daga kashi 17.3.
Sanarwar ta kuma ruwaito cewa, za a cire haraji baki daya kan wasu nau'ikan madara da kunzugun yara, inda kayayyakin sanyi na ulu da wasu kayan abincin albarkatun ruwa su ma za su samu raguwar harajin.
Wannan tsarin zai shafi jimilar kayayyaki 187.
Ma'aikatar ta ce raguwar kudin haraji ya mai da hankali ne kan inganci da wasu nau'ikan kayayyaki da ba a iya samar da su a cikin gida ba, domin ba masu saye damar zabi tare da inganta tsarin samar da kayayyaki a cikin gida.
Gwamnati na kara karfafa shigo da kayayyakin masarufi ne domin biyan bukatun cikin gida. (Fa'iza Mustapha)