Wata sanarwa da hukumar ta CBRC ta fitar a jiya a shafinta na yanar gizo, ta ce za a sauya matakan da ake dauka yanzu haka, ta yadda ka'idojin da ake bi wajen baiwa bankunan waje, da na hadin gwiwa damar zuba jari a kasuwannin kasar ta Sin za su saukaka.
Hakan dai a cewar CBRC ya biyo bayan sanarwa mai kunshe da amincewar hakan ne da aka fitar tun cikin watan Maris. Kaza lika sanarwar ta bayyana cewa, hukumar sa ido ga sha'anin bankunan kasar Sin za ta saukaka ka'idojin samar da lasisi ga bankunan ketare, ko na hadin gwiwa, wajen gudanar da hidimomi da suka hada da cinikayyar takardun basussuka, da ba da sauran shawarwari na cinikayya. (Saminu Hassan)