in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bam ya hallaka mutane 13 a wata kasuwa a Najeriya
2017-12-03 12:35:42 cri

Wasu tagwayen boma bomai sun hallaka mutane 13 da kuma jikkata wasu mutanen 53 a kasuwar Biu dake arewa maso gabashin Najeriya a ranar Asabar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan yankin Victor Isuku ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce wasu 'yan kunar bakin wake mata biyu ne suka kaddamar da harin a kasuwar ta Biu mai cinkoson jama'a.

Isuku ya ce, bam na farko ya tashi ne da tsakar rana, sannan bam na biyu ya tashi 'yan mintoci kadan bayan tashin na farkon a wajen kasuwar.

Hukumar 'yan sandan ta ce, ana zargin kungiyar 'yan ta'adda na Boko Haram da daukar alhakin kaddamar da harin. Kungiyar 'yan ta'addan ta hallaka sama da mutane dubu 20 a Najeriya tun bayan fara kaddamar da hare harenta a shekarar 2009.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China